On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

'Yan Bindiga Sun Sako Ukku Daga Cikin Dalibai Mata Na Makarantar Yawuri Da Suka Sace

Ukku daga cikin ragowar daliban nan Mata guda bakwai na makarantar ‘Yan Mata ta Birnin Yawuri a jihar Kebbi da suka rage tsare a hannun ‘yan bindiga sun shaki Iskar ‘Yanci.

Shugaban kungiyar  Iyayen  yaran  da aka sace,  Malam  Salim  Kaoje  ya  tabbatar da  cewar,  ‘Yan matan da aka saki  sun isa  birnin Kebbi da  yammacin  ranar Litinin.

Malam Salim  ya  ce  sun biya wasu makudan kudi domin sakin hudu  daga  cikin daliban mata  dake  tsare  a hannun  ‘yan bindigar  bayan sun sayar  da  wasu  kadarorinsu, tare da gudunmuwar da suka samu  daga  wasu  ‘Yan Najeriya da dama  domin  ganin an saki yaran.

Idan ba’a  manta,’Yan Bindiga sunyi awon gaba  da Dalibai  mata  96  na makarantar  Birnin Yawuri dake  jihar  Kebbi, a  yayin wani hari da suka kai ranar  17 ga watan  yunin 2021, yayin da koda  a watan da  ya  gabata  sai da aka saki  hudu  daga cikinsu.