On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da 'Dan Kasuwa A Jahar Jigawa

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari kauyen Kwadabe da ke karamar hukumar Kiyawa a jahar Jigawa inda suka yi awon gaba da wani dan kasuwa Alhaji Lawan Garba mai shekara 50 a duniya.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Shiisu Adam, shi ne ya tabbatar da hakan ga jaridar daily trust a wata tattaunawa ta wayar tarho a daren ranar Litinin.

Ya ce ’yan sandan sun samu labarin harin ne ta hannun wasu 'yan kasa masu kishi da ke kauyen da misalin karfe 10 na safe a ranar ta litinin, kuma nan take jami’ansu suka bazama  tare da fara bincike kan al'amarin inda suka tabbatar da sahihancin garkuwa da dan Kasuwar.

 Adam ya ce masu garkuwa da mutanen sun tafi da wayoyin dan kasuwar guda 2. 

Jigawa Map

Shiisu ya tabbatar da cewa ‘yan sanda ba za su ja da baya ba a kokarin da suke yi na kama masu laifi sannan  kuma gurfanar da su a gaban kotu.

 Daga nan sai ya yi kira ga al’ummar jihar Jigawa da su rika sanar da jami’an tsaro cikin gaggawa idan suka ga abubuwan da ba a saba gani ba ko wani abu sake da alamar tambaya