On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

'Yan Fashin Daji A Jahar Zamfara Sun Daina Karbar Tsaffin Takardun Naira A Matsayin Kudin Fansa

Wasu da ake zargi yan tada kayar baya ne sunyi garkuwa da mutane hudu da suka hada da wani mutum da babbar mace sai yara kananan yara guda biyu a kauyen kolo da ke karamar hukumar Gusau na jihar Zamfara.

Masu garkuwan sun bukaci a biya naira miliyan goma a matsayin kudin fansa,yayin da sukayi watsi da tsofaffin kudi wajen biyan kudin fansar.

Masu garkuwan sun bukaci a biya naira miliyan goma a matsayin kudin fansa,yayin da sukayi watsi da tsofaffin kudi wajen biyan kudin fansar.

Wani mazaunin kauyen, Muhammad Ibrahim, yace daga bisani ‘yan bindigar sun rage kudin fansar zuwa naira miliyan biyar,inda ya kara da cewa mutanen kauyen suna kokarinsu na ganin sun hada kudin fansar ‘yan uwansu.

Kazalika masu garkuwar sun aikewa al’ummar kauyen cewa bazasu karbi tsaffin kudi ba inda suka kara da cewa zasu cigaba da ajiye mutanen a wajen su har sai an fito da sabbin kudi na naiara a Najerita cikin  watan Disamba dake tafe.