On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

'Yan Kasuwa Na Kirga Asara Bayan Direbobin Manyan Motoci Sun Bude Titin Zaria A Kano

‘Yan kasuwa a Kano na ci gaba da kirga asarar da suka yi kwanaki bayan rufe hanyar Zaria zuwa Kano wanda hakan ya kawo cikas ga harkokin sufuri.

Idan dai za a iya tunawa, a karshen makon da ya gabata ne direbobin tanka suka tare hanyar Zaria zuwa Kano na tsawon kwanaki uku, biyo bayan zargin kashe daya daga cikin mambobinsu da wani soja ya yi.

Da yake tsokaci akan al’amarin, wani dan Kasuwar kayan gwari a ‘yan Kaba Umar Ibrahim yace mambobinsu sun yi asarar kimanin Naira milliyan 40 sanadiyar rufe titin.

Ibrahim ya ce galibin kayayyakin da ke kan hanyar zuwa kasuwa sun lalace ne sakamakon hana zirga-zirgar ababen hawa da direbobin tireloli suka yi a kan hanyar domin nuna fushinsu  kan cin zarafin jami'an tsaro..

Ya kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da ta Jiha da su yi abin da ya kamata tare da dakile afkuwar irin wannan a nan gaba, yayinda ya  roki a duba irin asarar da manoman suka yi domin su koma gona.

Shi kuwa, Shugaban kungiyar masu kiwon Kaji a Najeriya reshen jihar Kano Umar Kibiya Usman ya bayyana fargabar  cewa farashin kaji dama sauran kayayyaki ka iya tashi daga yadda suke a yanzu a sakamakon takaddamar toshe babbar hanyar Zaria zuwa Kano da direbobi sukayi abaya-bayan nan.

Da yake ganawa da Arewa Radio, Usman yace koda yake har yanzu suna kan kididdigar  sanin adadin asarar da suka fuskanta, amma mambobin kungiyar guda 3 sun bayyana cewa sunyi asarar kaji da dama a dai dai lokacin da aka rage samun Kajin a cikin jihar Kano.

A nasa bangaren shugaban gamayyar kungiyoyin masu safarar kayayyakin abinci da dabbobi a Najeriya  Dr Mohammed Tahir, yace dabobi da dama sun mutu, a yayin da wasu daga cikin mambobin kungiyar suka yanka dabobin su a kan hanya sanadiyar rufe titin na Kano zuwa Zaria.

 

More from Labarai