On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

‘Yan Kudu Maso Yamma Su Hakura Da Takarar Shugabancin Najeriya – Afenifere

Jagoran ya bayyana hakan ne cikin wata zantawa  da jaridar Punch ranar Talata

Shugaban majalisar tuntuɓa ta ƙabilar Yarabawa, Afenifere, Cif Ayo Adebanjo ya shawarci masu neman takarar shugabancin Najeriya daga yankin kudu maso yamma da su haƙura da burinsu.

Shugaban ƙungiyar  ta Yarbawa  ya ce ya kamata 'yan takarar yankin nasu kamar Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo su bar wa 'yan ƙabilar Igbo don samar da shugaban ƙasa na gaba a 2023.

Jagoran ya bayyana hakan ne cikin wata zantawa  da jaridar Punch ranar Talata, yana mai cewa "rashin adalci ne ɗan kudu maso yamma ya zama shugaban ƙasa bayan Olusegun Obasanjo ya mulki Najeriya shekara takwas, sannan kuma Yemi Osinbajo zai shekara takwas a muƙamin mataimakin shugaban ƙasa".

Sai dai kuma dattijon mai shekara 94 ya ce "dole ne a kyautata ƙasar kafin Najeriya ta samu sabon shugaba".