On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

'Yan Kwadago A Najeriya Na Neman Naira Dubu Dari Biyu Amatsayin Mafi Karancin Albashin Ma'aikata

Kungiyar kwadago ta TUC tayi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya kara mafi karancin albashin ma’aikata a kasarnan zuwa Naira dubu 200 domin dakile illolin cire tallafin man Fetur.

Ya ce ya kamata a yi hakan kafin karshen watan Yuni domin aiwatar da dokar masana’antar man fetur, inda ya kara da cewa ya kamata a yi la’akari da daidaita abunda ‘yan kasa ke samu wajen rayuwarsu ta yau da kullum.

Shugaban kungiyar da kuma babban sakataren kungiyar ta TUC, Festus Osifo da Nuhu Toro, a wata sanarwa da suka sanyawa hannu, sun ce wadannan na daga cikin bukatunsu a cigaba da tattaunawa da gwamnati.

Osifo yace sun kuma bukaci a ci gaba da a koma tsohon farashin man Fetur yayin da ake ci gaba da tattaunawa.