On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

'Yan Majalissar Wakilai A Najeriya Sun Musanta Karbar Tallafin Rage Radadi Na Milliyan 100 Kowannensu

Majalisar wakilai ta yi watsi da wata sanarwa daga mataimakin sakataren kungiyar kwadago ta kasa NLC, Christopher Onyeka cewa kowanne mamba ya samu Naira milliyan 100 amatsayin tallafi.

Shugaban kwamitin majalisar kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Akin Rotimi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Idan za’a iya tunawa Onyeka ya yi ikirarin a ranar Talata cewa bangaren zartaswa ya baiwa kowane dan majalisar tarayya Naira miliyan 100 amatsayin tallafi.

Da yake mayar da martani, Rotimi ya ce wannan ikirari ba shi da tushe balle makama.

Ya nuna shakku kan ko Onyeka na wakilcin kungiyar NLC a hukumance kan ikirarin, ya kara da cewa duk da haka yana da muhimmanci a gyara irin wadannan bayanai.