On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

‘Yan Najeriya Zasu Fara Biyan Kanfanonin Sadarwa Harajin Sama Da Kaso 12 Bisa 100 Na VAT

KANFANONIN SADARWA A NAJERIYA

Yan Najeriya zasu fara biyana Harajin kaso 12 da digo 5 bisa 100 ga kanfanonin sadarwa dake kasar nan, A yayin da gwamnatin taraiyya ke shirin aiwatar da fara biyan kaso biyar bisa 100 na harajin kayayyaki ga kanfanonin sadarwa dake kasar nan.

Ministar Kudi Kasafi da kuma tsare-tsaren cigaban Kasa, Hajiya Zainab Ahmed ce ta baiyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da harajin , wanda kanfanonin sadarwa zasu fara biya.

Ministar ta baiyana cewa kaso biyar bisa 100 na harajin da kanfanonin sadarwar  zasu rika biya, yana bisa doron dokar tafiyar da harkokin kudi ta shekarar  2020, sai dai ba’a samu damar fara aiki da ita ba, sakamakon tattaunawar da gwamnati keyi da masu ruwa da tsaki.

Da yake nasa jawabin, Shugaban Kungiyar masu kanfanonin sadarwa ta kasa, Gbenga Adebayo, Yace matakin babu wanda zaifi shafa sai abokan huldar kanfanonin sadarwar.

More from Labarai