On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

'Yan Sanda A Jihar Imo Sun Gargadi Masu Shirin Kawo Cikas Ga Zaben Gwamna Dake Tafe

Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta gargadi kungiyoyin kwadago da su guji tursasa masu kada kuri’a a zaben da za a gudanar a ranar Asabar a jihar, tana mai cewa ba za ta zuba idanu akan duk wani shiri na kawo cikas ga zaben.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Henry Okoye, ya ce an jibge ‘yan sanda sosai a fadin jihar bayan tantance yanayin tsaro.

Da yake magana kan yajin aikin kungiyar kwadago, Okoye ya dage cewa kungiyoyin kwadago ba su da ikon da tsarin mulki ya ba su na dakatar da zabe, don haka ya gargadi shugabannin kungiyoyin da su guji tursasa masu zabe.

Dangane da barazanar kungiyar IPOB da kungiyar tsaro ta Gabas, kakakin ‘yan sandan ya ce rundunar ‘yan sandan za ta yi maganin duk wani mutum ko kungiyar da ke da ra’ayin aikata laifuka da nufin  kawo cikas a zaben.