On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

'Yan Sanda Sun Kama Matashi Da Ake Zargi Da Kisan Kishiyar Mahaifiyarsa Mai Juna Biyu Da Diyarta A Jihar Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Gaddafi Sagir mai shekara 20 a duniya, bisa zarginsa da dabawa kishiyar mahaifiyarsa Sukundireba tare da shake kanwarsa mai shekara 8 wanda yayi sanadiyar ajalinsu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da kama matashin ta  cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a karshen mako.

Kiyawa yace sun samu labari daga wani Sagir Yakubu daga unguwar  Rijiyar Zaki a Kano a ranar Asabar da ta gabata cewa ya dawo gida ya iske matarsa ​​mai juna biyu Rabi’atu Sagir, mai shekara  25 ta mutu a cikin jini, da diyarta, Munawwara Sagir, mai shekaru 8, an shaketa.

A cewar rundunar ‘yan sandan, Yakubu ya bayyana shakkunsa akan ko dansa Gaddafi zai iya aikata kisan.

An kama wanda ake zargin ne a wani kango yana kokarin tserewa daga Kano.

A yayin gudanar da bincike na farko, wanda ake zargin ya amsa cewa ya yi amfani da Sukundireba wajen dabawa kishiyar mahaifiyarsa yayin da ya shake 'Diyarta.