On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

'Yan Ta’adda Sun Halaka Malamin Kwalejin Zamfara Bayan Sun Karbar Naira Milyan Biyar

KIDNAPPERS

Masu Garkuwar da suka sace Malamin Kwalejin kimiyya da Fasaha ta Abdu Gusau dake jihar Zamfara mai suna Sanusi Halilu sun halakashi har lahira bayan sun karbi kudin fansa har naira milyan 5.

An sace Malam Sanusi Halilu wanda shine shugaban sashin kula da harkokin Dalibai na Makarantar,  tare da wasu mutane kimanin makwanni biyar da suka gabata a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Abuja, domin tattaro bayanan masu aikin hidimtawa kasar da aka tura zuwa makarantar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an biya  Masu garkuwa kudin ne a ranar Talatar data gabata a wani Daji dake kusa da kan hanyar Kaduna zuwa zariya a jihar Kaduna.

Yan Ta’addar sun tabbatar da mutuwarsa kasa da Kwana Daya bayan an biyasu kudin fansar, wanda hakan ke tabbatar da cewa sun jima da kashe shi tun a lokacin da ake tattaunawa  dasu.

A wani bangaren kuma Mutanen nan 29 da aka sace a lokacin da suke kan hanyar zuwa Daurin aure a  jihar Zamfara  sun kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane.

 

More from Labarai