On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Yan ta’adda Sun Kai Hari Shigen Binciken Ababen Hawa Na Dakarun Soji Dake Kusa Da Dutse Zuma A Abuja

HOTON DUTSE ZUMA

Rahotanni na baiyana cewa an halaka wasu wasu sojoji yayin da Mayakan Boko Haram suka kai farmaki wani shingen binciken dakarun sojoji da ke kusa da dutsen Zuma a jihar Neja, a daren jiya.

Wajen da abun ya faru wanda yake kusa da  garin Madalla  bashi da wani  nisa daga Zuba  dake  kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Wasu ganau ba jiyau ba sun   fadawa  manema  Labarai  cewa maharan sun isa wurin ne bayan  karfe  7 na dare, inda nan take suka bude wuta.

Sun  kara da cewa ‘yan ta’addar  sun kwace  ikon  yankin na kusan mintuna 30 sannan suka ci gaba da harbe-harbe  babu kakkautawa   kafin daga bisani su tunkari  babbar  hanyar zuwa  Kaduna

Sai dai kuma daga bisani  tawagar  jami’an yansanda  masu aikin sintiri  su isa  wurin da abun ya faru.

 

More from Labarai