On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

'Yan Ta'adda Sun Kone Wani Limamin Katolika A Jihar Neja

Da tsakar daren ranar Lahadi ne wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kona wani Rabaran Isaac Achi na majami’ar St. Peters da Paul Catholic a kan hanyar Daza a karamar hukumar Paikoro ta jihar Neja.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasi’u   Abiodun, ya fitar, yace ‘yan bindigar sun yi yunkurin shiga gidan Rabaran Achi  ne da misalin karfe uku na dare, amma suka fuskanci matsala inda daga bisani suka kona gidan.

Yace an harbe wani abokin aikin Rabaren din mai suna Father Collins a kafada yayin da yake kokarin tserewa.

Ya kara da cewa maharan sun tsere ne kafin isowar tawagar ‘yan sanda.

Sai dai an gano gawar  Isaac Achi  yayin da aka garzaya da Father Collins asibiti domin kula da lafiyarsa.

More from Labarai