On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

'Yan Tada Kayar Baya A Najeriya Sun Fara Shiga Wani Hali Saboda Karancin Maboya Da Abinci Da Kuma Makamai

Rahotanni sun daruruwan mayakan Boko Haram da iyalansu sun bar sansanoninsu, sakamakon ambaliyar ruwa da ta yi barna a yankunansu, al’amarin da ya tilasta musu yin kaura zuwa wasu wuraren da ba a amince da su ba a gefen dajin Sambisa.

An rawaito cewa ambaliya da kogin Yedzaram ya yi ta shafi sansanonin ‘yan ta’adda da dama a Sheuri da mazabar Kumshe  da Gaizuwa a ranar Lahadi.

Idan ba a manta ba a jiya  mun bayar da rahoton yadda ‘yan tada kayar baya 70 suka nutse a ruwa bayan dakarun soji sun  hallaka sama da mutum 200 daga cikinsu da suka hada da kwamandoji biyar biyo bayan hari ta sama a karshen mako.

Baya ga amabaliyar kuma, karancin makamai, da abinci ma na daga dalilan tserewar ta su.

A hannu guda kuma, wani Kwamnadan kungiyar Goni Farooq ya mika wuya ga rundunar soji a Karamar Hukumar Bama da ke Jihar Borno a ranar Lahadi.

Wata majiyar sirri ta bayyana cewa Kwamnadan ya kuma mika makamai da suka hada da AK47 45, da harsasai, da manyan bindigogi, da na`urar samar da lantarki mai amfani da hasken rana, da sutura da sauran kayayyaki.