On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

'Yan Wasa Gabriel Jesu Da Countinho Ba Zasu Buga Wasan Sada Zumunci Da Brazil Zata Yi Da Kasashen Ghana Da Tunisia

Rahotanni na baiyana cewa babu sunayen yan wasa Gabriel Jesus da Philippe Coutinho daga cikin jerin 'yan wasan da kasar Brazil zata buga wasan sada zumunci tsakaninta da kasashen Ghana da Tunisia, a yayin da kasashen ke shirye-shiryen tunkarar gasar cin kofin duniya.

Zakarun gasar cin kofin kwallon kafa na  duniya sau biyar za su kara da Ghana a Faransa ranar 23 ga watan Satumba kafin su kara da Tunisia kwanaki hudu bayan fafatawarsu da kasar Ghana

Dan wasa Gabriel Jesus, wanda ya taka rawar gani a kakar wasa ta  bana tun lokacin da ya koma kungiyar Arsenal daga Manchester City, ya buga wa Brazil wasa sau 11 a gasar cin kofin duniya ba tare da ya zura kwallo a raga ba.

Za  dai a fara gasar  cin kofin kwallon kafa ta duniya a  Qatar ranar 20 ga watan Nuwambar bana.

More from Labarai