On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Za'a Bude Kwalejojin Utopia Da Savannah Watanni 9 Bayan Rufewa A Jihar Kano

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin bude sake kwalejin kimiyya da harkokin Lafiya na Utopiada Savannah da ke kananan hukumomin Wudil Nassarawa.

Umurnin ya biyo bayan gamsuwa da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na bin ka’idojin tafiyar da kwalejojin kimiyyar lafiyar.

Hakan ya biyo bayan umarnin da kwamitin da gwamnatin jihar Kano ta kafa na kula da ayyukan irin wadannan kwalejoji ya bayar, wanda ya kunshi babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kano Hon Auwal Abdullahi Yola.

Idan za’a iya tunawa an rufe kwalejojin Utopia da Savannah a cikin watan Fabrairu na shekarar 2022.

More from Labarai