On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Za'a Cigaba Da Amfani Da Tsaffin Takardun Kudi Na Naira A Najeriya - CBN

Babban Bankin kasa CBN na gargadin kin amincewa da duk wata takardar kudi ta banki saboda fargabar cewa tsofaffin takardun kudi na iya daina shiga kasuwa nan da watan gobe na  Disambar 2023.

A wata sanarwa da aka  fitar ranar Laraba mai dauke da sa hannun mai magana da yawun bankin, Isah Abdulmunin, CBN ya ce bai bayar da umarnin daina amfanin da tsoffin takardun kudin na Naira ba.

Sanarwar ta kara da cewa, an umarci dukkanin rassan CBN da su ci gaba da fitar da tsofaffin takardun kudi a adadi mai yawa ga bankuna don ci gaba da zagayawa.

Idan ba a manta ba a watan Maris ne kotun koli ta bayar da umarnin ci gaba da aiki da tsofaffin takardun kudi na Naira 200 da 500 da kuma Naira dubu 1 har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, bayan da jihohi 16 suka shigar da kara domin kalubalantar sahihancin bullo da sabuwar manufar chanjin takardar kudi.