On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Za'a Cigaba da Rijistar Katin Zabe a Jihar Imo Bayan Harin da 'Yan Bindiga suka Kaiwa Ma'aikatan INEC

A cikin wata sanarwa da mai magan da yawunsa Oguwike Nwachukwu ya fitar...

Rahotanni na nuni da cewa Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta janye matakin dakatar da aikin cigaba da Rijistar zabe a jihar Imo.

Idan za’a iya tunawa dai an dakatar da aikin biyo bayan harin da ‘yan bindiga suka kaiwa ma’aikatan hukumar ta INEC dake Rijistar zabe.

Sai dai gwamnan jihar ta Imo Hope Uzodinma ya sanar da cewa za’a cigaba da Rijistar katin zaben daga yau Litinin.

A cikin wata sanarwa da mai magan da yawunsa Oguwike Nwachukwu ya fitar, gwamnan ya sanar da hakan ne fadar gwamnatin jihar bayan kammala Addu’oin Majami’a a karshen mako..

Har yanzu hukumar zabe INEC bata tabbatar da wannan mataki ba kawo lokacin hada wannan rahoto.

More from Labarai