On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Za'a Kara Harajin Taba Sigari Zuwa Kashi 50% A Najeriya

Gwamnatin tarayya za ta kara harajin taba sigari daga kashi 30 cikin 100 zuwa kashi 50 cikin 100 a wani mataki na dakile shan taba a Najeriya

Shugaban sashen hana shan taba sigari na sashin cututtuka marasa yaduwa na ma’aikatar lafiya ta tarayya Dr Mangai Malau shine ya bayyana hakan a ranar Talata a taron masu bada shawara kan kasafin kudin yaki da taba sigari na kasa a Abuja.

Malau ya ce a halin yanzu, gwamnatin tarayya ta sanya harajin kashi 30 cikin 100 kan kayayyakin da suka shafi  sigari amma burinta shi ne harajin ya karu zuwa kashi 50 cikin 100 domin cika ka'idojin hukumar lafiya ta duniya.

A cewarsa, dole ne a samar da kudaden da za’a dakile taba sigari musamman ta hanyar  haraji sannan kuma akwai bukatar masu ruwa da tsaki su yi amfani da matakan haraji daidai gwargwado idan har ana son magance matsalolin da suka shafi taba sigari a kasarnan.