On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Za'a Samar Da Motoci Sama Da Milyan 11 Masu Amfani Da Gas

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin samar da motoci miliyan daya masu amfani da Gas nan da shekarar 2027.

A cewar mashawarcin shugaban kasa na musamman kan harkokin samar da dabarun cigaban kasa,  Toyin Subaru, ya  ce  motocin zasu temaka  wajen saukaka yanayin zirga-zirga a kasar nan.

Ya kuma baiyana cewar  ana saran samfurin motocin sama  da guda  dubu 11  zasu fara aiki a cikin wannan makon.

Subaru ya ba da tabbacin cewar fara  sufurin motoci masu amfani da makamashin gas, zai temaka wajen karya farashin gas  zuwa naira 230 akan kowanne  kilogiram daya.