On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Zaben 2023: AU Zata Turo Tawagar Sanya Idanu A Zaben Najeriya

Hukumar kungiyar tarayyar Afirka ta sanar da cewa za ta turo tawagar masu sa ido 90 zuwa Najeriya domin gudanar da manyan zabukan 2023.

Tsohon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta shine ke jagorantar tawagar kungiyar Tarayyar ta Afirka, wanda ya taimaka wajen kulla yarjejeniyar kawo karshen yakin da aka shafe shekaru biyu ana yi a arewacin kasar Habasha, kuma ke shiga tsakani a rikicin gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

Kungiyar ta AU tace makasudin wannan tawaga ita ce samar da tabbataccen sanya idanu ba tare da nuna son kai ba game da zaben, da ba da shawarwari ga duk wani ci gaba a zabukan da za a yi nan gaba da kuma nuna goyon bayan AU wajen tabbatar da dimokuradiyya da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a Najeriya. .

Kusan mutane miliyan 100 ne za su kada kuri’a domin zaben wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari, wanda zai sauka daga mulki bayan wa’adi biyu a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalar rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki.