On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

ZABEN 2023:: Babu Sunan Bashir I Bashir A INEC Amatsayin 'Dan Takarar Gwamna A Kano - LP

Jam’iyyar Labour a jihar Kano ta yi watsi da ikirarin cewa Bashir Ishak-Bashir, wanda ya koma jam’iyyar APC, shi ne dan takararta na gwamna.

 

Shugaban jam’iyyar Labour  a jihar, Alhaji Mohammed Raji, ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Litinin cewa, sunan Ishak-Bashir bai taba shiga shafin INEC ba a matsayin dan takarar jam’iyyar a Kano.

Raji yace Bashir ya zo jam’iyyar shi kadai ya bari shi kadai.

Ya kuma cewa  tsarin jam’iyyar ya ci gaba da kasancewa tare da dukkan ‘yan takararta da zasu fafata a zabukan da ke tafe.

Hakan na zuwa ne yayinda rikici ya barke a jam’iyyar Labour a yankin Kudu-maso-Yamma yayin da shugabanninta suka sanar da rushe daukacin tsarinta na yankin zuwa jam’iyyar APC.

Shugabannin jam’iyyar sun kuma bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu.

Shugaban jam’iyyar Labour  ta Kudu-maso-Yamma, Mista Omotoso Banji, ya shaidawa manema labarai a Akure cewa, shugabannin jam’iyyar sun yanke shawarar ficewa ne saboda jam’iyyar Labour ba ta da karfin da za ta iya lashe zabukan dake tafe.

Sai dai shugabar jam’iyyar Labour a jihar Ondo, Mrs Remilekun Ojo, ta yi watsi da rushewar tsarin jam’iyyar, inda tace wasu mutane goma sha biyu ne suka dauki wannan matakin da suka yi ikirarin cewa sune yankin Kudu-maso-Yamma na jam’iyyar.