On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Zaben 2023 Nada Muhimmanci Ga Nahiyar Afrika - Birtaniya Ta Gargadi Najeriya

Babbar jami’ar Birtaniya a Najeriya, Catriona Laing, da kungiyar kasashe rainon Ingila dake bibiyar yanayin da ake ciki kafin zabe a Najeriya sun yi kira ga jam’iyyun siyasa da alkalan zabe da su tabbatar da cewa babban zaben shekarar 2023 ya kasance cikin aminci da kwanciyar hankali da lumana.

Da take jawabi yayin wata ganawa da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP na kasa a Abuja a ranar Laraba, Laing ta ce Burtaniya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen sanya takunkumi kan duk wani mutum ko kungiyar da su ka yi tashin hankali a zabe.

Ta  ce Burtaniya ta damu matuƙa kan abubuwan da suka faru na baya-bayanan, ciki harda rikice-rikice 52 masu alaƙa da zaɓe a jihohi 22.

A wata ganawa ta daban da Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, Mahmood Yakubu, kungiyar ta jaddada bukatar Najeriya ta daidaita da zabuka, inda ta bada misali da tasirin da kasarnan ke da shi a nahiyar Afirka a matsayin dalilin da ya sa ba’a bukatar ganin wata gazawa.

Har ila yau, Jami'ar ta ce suna ta tattaunawa da masu ruwa da tsaki, ciki harda Inec, da kungiyoyin fararan-hula da 'yan siyasa domin tabbatar da sahihin zaɓe cikin kwanciyar hankali a Najeriya.

Shugaban na INEC, Farfesa Yakubu ya tabbatar wa kasashen duniya cewa hukumar za ta gudanar da sahihin zabe a shekarar 2023.