On Air Now

Off Air

Noon - 6:00pm

ZABEN 2023: Yawaitar Ayyukan Tarzomar Siyasa Na Kara Barazana Ga Rayuwar Al’ummar Jihar Kano – Kwamitin Zaman Lafiya

Kwamitin zaman lafiya na Kano ya bayyana damuwa akan karuwar Barazanar da ayyukan dabbar siyasa ke yi a sassan jihar zabanin fara manyan zabukan 2023.

Ta cikin wata sanarwa dauke da sahannun Comrade Ibrahim Abdullahi Waiyya wadda aka aikowa Arewa Radio, kwamitin yace, ya lura da cewa, an wargaza  yarjejeniyar zaman lafiya ta Kano da ‘yan takarar gwamna 8 na jihar suka rattabawa hannu, ta yadda wasu magoya bayan jam’iyyun siyasa ke arangama a ‘yan kwanakin nan.

Kwamitin ya bada misali akan abubuwan da sukafaru yayin tarukan siyasa a kananan hukumomin Dambatta da Makoda da Rimin Kebe  da Mandawari da Rigiyar Lemo da Larabar Abasawa da  Dawakin Kudu and Tudun Wada.

Wannan mummunan acewar kwamitin yana barazana ga zaman lafiya da tsaro a jihar Kano.

Rikicin da ya faru a unguwar Rimin Kebe da ke karamar hukumar Nassarawa,  ya yi sanadiyyar mutuwar wani yaro da baiji ba bai gani ba wanda ake zargin magoya bayan dan takarar majalisar wakilai ne sukaaikata, acewar sanarwar.

Kwamitin yace irin hakan ba wai kawai hadari ne ga rayuwar ‘yan Kano ba, ya sabawa dokar zabe ta 2022 da aka yi wa gyaran fuska da kuma wargaza kokarin kawo zaman lafiya da tsaro a Jihar.

Saboda haka kwamitin ya bukaci daukar kwararan matakai daga hukumomin tsaro  ba kawai kan masu aikata laifin ba har ma da masu daukar nauyinsu.

Kwamitin zaman lafiya na Kano yace ya damu matuka da irin wadannan matsaloli da suka kunno kai ga zaman lafiya da tsaron jihar, saboda yake kira da babbar murya ga shugabannin jam’iyyun siyasar da abin ya shafa, da su mutunta ka’idoji da kuma yarjejeniyar zaman lafiya da duk suka rattabawa hannu domin kare lafiyar al’umma da  tsaro ga al’ummar Kano.

Har Ila yau, kwmaitin ya  kara kira ga kafafen yada labarai da su daina yin shiru akan irin wadannanan rahotanni hanyar fallasa sunayen jam'iyyun siyasa da ke da hannu wajen yada irin wannan tashin hankali da  sunayen wadanda abin ya shafa da kuma yadda al’amarin ya faru.

Dagan kwamitin ya yabawa kokarin kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, akan yawan kama  wadanda suka kai wasu munanan hare-hare, da kwace wasu muggan makamai tare da gurfanar da su gaban kuliya. Sai dai kwamitin na zaman lafiya ya roki kwamishinan da ya kama tare da gurfanar da manyan masu daukar nauyin wannan rikici a duk jam’iyyar da suke domin magance karuwar tashe-tashen hankula na  siyasa a jihar.