On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Zamu Gudanar Da Zanga-Zanga Tare Da Kauracewa Shiga Aji A Jami'oin Gwamnati - ASUU

Kungiyar Malaman Jami’o’I kasa ASUU ta shirya gudanar da zanga-zangar kwana 1 a fadin kasarnan domin nuna rashin amincewa da yadda Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da tsarin ba aiki, ba biyan albashi  ga malaman jami’o’i a Najeriya.

 

Za’a gudanar da zanga-zangar ne a matakan rassan kungiyar da ke  jami’o’in gwamnati a fadin kasarnan, kuma za’a ayyana ranar a matsayin ranar da ba shiga Aji.

Wani mamba a majalisar zartaswar kungiyar a kasa ya tabbatar da hakan a wata zantawa da manema labarai a ranar Lahadi.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto an gaza samun, Shugaban kungiyar ta ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, sai dai shugaban na ASUU shiyyar Kano Abdulkadir Muhammad yace sun zabi ranar alhamis domin aiwatar da zanga-zangar.

Hakan na zuwa ne a lokacin da shugaban kungiyar iyaye da malamai ta a kasarnan PTA, Haruna Danjuma, ya yi Allah wadai da biyan rabin albashi ga  malaman jami’o’in gwamnati da gwamnatin tarayya ta yi.

‘Danjuma wanda ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai, yace yarjejeniyar farko da bangarorin biyu suka kulla ta amince  za a biya cikakken albashin watannin da malaman ke yajin aiki zuwa wani lokaci kalilan  bayan an dakatar da yajin aikin..

A cewar ‘Danjuma, matakin da gwamnati ta dauka ba iya rashin adalci ba ne,  zai iya haifar da wani yajin aikin.

Mambobin kungiyar malaman jami’o’in sun koka kan biyan rabin albashin da gwamnatin tarayya ta yi a watan Octoba duk kuwa da matakin da suka dauka na janye yajin aikin da suka shafe watanni takwas suna yi kamar yadda kotu ta bayar da umarni.