On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Zamu Tabbatar Da Samuwar Wutar Lantarki A Najeriya Zuwa Megawatt Dubu 25 - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace gwamnatinsa ta tabbatar da karuwar samar da wutar lantarki zuwa megawatt dubu 25 a Najeriya.

Ya bayyana haka ne yayin taron sake bibiyar  ayyukan ministoci karo na uku a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Taron na bana, mai taken haɓaka tsaro da yaki da cin hanci da rashawa da sauya Tattalin Arziki’, na da nufin duba ci gaban da gwamnatin ta samu tun daga shekarar da ta gabata.

Ya kuma yi alkawarin cewa gwamnati mai ci za ta ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa da kuma hukunci akan manyan laifuka cikin gaggawa.

Yayin da yake jawabi a taron tsohon shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, ya bukaci 'yan Afirka da su sake tunani kan yadda ake gudanar da siyasa a nahiyar.

More from Labarai