On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Zan Sake Fasalin Tsaro A Najeriya Idan Aka Zabeni - Kwankwaso

‘Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya bayyana kudirinsa na sake fasalin harkokin tsaro a Najeriya

Tsohon ministan tsaro Sanata Rabiu Kwankwaso, kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP shine ya bayyana hakan a karshen mako ta cikin wani shiri kai tsaye da gidan talabijin na Channels ya shirya a Abuja.

 

A cewarsa, matakan sun hada da kafa ‘yan sandan jihohi a fadin tarayya, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada.

Kwankwaso yace ‘yan Najeriya suna da sha’awar sake fasalin  tsaro a kasa inda gwamnatinsa idan aka zabe shi za ta bi tsarin da ya dace wajen ganin kowa ya samu tsaro.

Haka kuma Dole ne a yanke hukunci kan tabarbarewar tsaro irin wadda ta haifar da harin da aka kai a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja ranar 5 ga watan Yuli.

Ya dage akan cewa babu wanda ya isa ya yi karfin doka a Najeriya.