On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Hukumar Hisbah a jihar Jigawa ta lalata kwalaben giya a watan Ramadan

Yace sun kama jarkokin burkutu da aka haɗa a matsayin giya.

 

Hukumar Hisbah a jihar Jigawa ta lalata kwalaben giya dub 1 da 426 da aka kama a wasu kananan hukumomi biyu na jihar.

Kwamandan hukumar Ibrahim Ɗahiru shine ya bayyana haka  ranar  Alhamis a Dutse babban birnin jihar.

Yace sun kama jarkokin burkutu da aka haɗa a matsayin giya.

Sauran barasar da aka fasa ta kwalba an kama ta a wuraren da su ka haɗa da mahaɗar holowa, Otel, da kuma wasu wurare daban-daban.

A ranar 3 ga watan Afrilu da mu ke ciki aka kama wasu mutane 14 da kwalaben giya 177 sai wata jarka makare da burkutu a  ƙaramar hukumar Gumel ta jihar.

An kuma  kama kwalaben giya 1,249 da wasu kwalaben giya waɗanda babu komai a ciki guda 143 sai wata mota wadda ya ce an kama mammalakin giyar a Dutse babban birnin jihar.

Hukumar ta godewa al'ummar jihar Jigawa bisa hadin kai da su ke bayarwa musamman wajen tabbatar da bin dokokin Hisbah.