On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

An Kama Wani Da Ake Zargi Da Hada Baki Da Yan Bindiga Wajen Halaka Mahaifinsa

YAN BINDIGA

Rundunar yansandan jihar Yobe ta tabbatar da cafke wani matashi mai shekaru 20 a duniya mai suna, Yahaya Sa’idu, wanda ake zargin ya hada baki da yan bindiga domin halaka mahaifinsa mai suna Sa’idu Oroh.

Kakakin rundunar yansandan jihar DSP, Dungus Abdulkarim ne ya baiyaan haka ga manema Labarai a birnin Damaturu, ya ce an kama wanda ake zargin ne a Gujba a ranar Litinin data gabata.

Kazalika yace wanda ake zargin ya dauko hayar  yan ina da kisa wanda sune suka bindiga mahaifin nasa har lahira a gidansa dake kauyen  Pompom a ranar  20 ga watan Augustan bana.

Mai magana da yawun rundunar yansandan jihar, Ya ce a yanzu haka rundunar tana kan laluben sauran wadanda suka cika wandonsu da iska, inda ya bada tabbacin cewa nan bada jimawa ba zasu fada komarsu.