On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

An Sace 'Yar Surikar Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa

FARFESA ANGO ABDULLAHI

Wata Daya bayan da ‘yan bindiga suka saki Dan gidan Dattijon Arewa Farfesa Ango Abdullahi , A yanzu haka yan bindigar sun sake sace ‘Yar Sirikar Shugaban kungiyar Dattawan Arewa.

Farfesa Ango Abdullahi ya tabbatar da haka ne a ranar Laraba, Yace an dauke matar ne tare da yaranta hudu.

Wata majiya ta shaidawa jaridar daily trust cewa, Maharan sun   afkwa garin Yakawada dake cikin karamar Giwa ta jihar Kaduna, a daren Talata  inda ka tsaye suka tunkari  gida Dagacin garin Alhaji Rilwanu Saidu.

A yanzu haka mutane ukku da suka ji raunika  a sakamakon harin suna karbar magani a asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Dan Farfesa Ango Abdullahi  na daga cikin fasinjojin jirgin kasa 60   da  yan Ta’adda suka sace a cikin watan maris din bana, amma daga bisani an sako shi wata daya  da ya  gabata.

 

More from Tsaro