On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Maharan jirgin kasan Abuja-Kaduna sun sake sakin Video

Cikin Fasinjojin akwai wani mutum da ake kyautata zatton dan Asia ne da kuma

‘Yan ta’ada da sukayi awon gaba da Fasinjojin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna sun sake sakin wani Video da ya nuna  mutanen da sukayi garkuwa da su.

Cikin sabon Vidiyon na minti 2 akwai kimanin ‘yan bindiga 10 da suka kewaye fasinjojin da aka tilastawa yin magana.

Cikin Fasinjojin akwai wani mutum da ake kyautata zatton dan Asia ne da kuma wata ‘Dalibar  jami’ar jihar Kaduna da suka roki gwamnati ta kubutar da su.

A ranar Larabar makon jiya ne dai ‘yan ta’adar suka saki Video na farko inda sukayi barazanar hallaka mutanen dake hannunsu muddin gwamnatin tarayya ta gaza biyan bukatunsu sai dai ba su zayyana bukatun ba, koda yake sunce gwamnati ta san abunda suke bukata.