On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Mutane Biyar Ne Aka Halaka Yayin Harin Da Aka Kaiwa Sanata Ifeanyi Ubah

SANATA IFEANYI UBAH

Rundunar Yansandan jihar Anambra ta tabbatar da mutuwar mutane biyar wadanda yan bindiga suka halaka a lokacin kaiwa ayarin sanata mai wakiltar Anambra ta Kudu, Ifeanyi Ubah hari a ranar Lahadin data gabata.

Kakakin rundunar  yansandan jihar Tochukwu Ikenga ne ya baiyana haka a ranar  Litinin , Yace  mutanen sun hada  jami’an yansanda  biyu da kuma  wadansu farar  hula  ukku.

Ya kara  da cewa  baya ga mutanen da  ‘yan bindigar suka halaka, kazalika yanzu haka akwai  jami’an yansanda biyu dake samun kulawa  sakamakon raunikan da suka samu.

Duk wani kokarin na jin tab akin mai magana da yawun  sanata Ubah, Mister Kameh Ogbonna  yace tura, Wanda  ya baiyana cewa  ba dan uban gidan nasa  na a cikin mota  mai sulke ba, tuni  labari ya riga ya canza.

More from Tsaro