On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Yan Bindiga Sun Sace Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar A Jihar Delta

Frank Esiwo

Rundunar yansandan jihar Delta, Ta tabbatar da Sace Mataimakin shugaban karamar hukumar Isoko ta Arewa mai suna Frank Esiwo.

Rahotanni sun baiyana cewa, anyi awon gaba da  da mataimakin shugaban karamar hukumar ne akan hanyarsa ta zuwa garin Patani lokacin da masu garkuwar suka tafi dashi a garin Ogor dake cikin karamar hukumar Ughelli ta arewa a ranar Lahadi.

Kakakin rundunar  yansandan jihar Edafe Bright ya tabbatar da faruwar lamarin, a yayin da jami’an yansandan ke kokarin ganin an kubutar da shi cikin salama.

Majiyarmu ta tabbatar da cewa masu garkuwar  sun bar mota da wayar mataimakin shugaban karamar hukumar a wajen, kuma har yanzu babu wanda suka tuntuba daga cikin iyalansa kawo yanzu da muke baku labarin.

More from Tsaro