On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

‘Yan sanda a jihar Katsina sun dakile harin ‘yan ta’adda

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta dakile harin da ‘yan ta’adda suka kai kauyen Gago da ke karamar hukumar Dutsinma a jihar.

‘Yan ta’addan wadanda adadinsu ya kai kimanin 40, sun kai farmaki kauyen ne da  karfe 1 na rana, inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi, kuma sunyi awon gaba da shanu 50 na wani Alh. Ibrahim Maikudi.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah ya fitar, ta ce ‘yan sandan sun yi artabu da ‘yan bindigar inda sukayi nasarar dakile harin tare da kashe daya daga cikin ‘yan ta’addan. 

A cewar Isah, da yawa daga cikin ‘yan ta’addan sun tsere da raunukan harbin bindiga, yayin da ‘yan sanda suka kwato shanu 50  da kuma bindigar AK 47 guda daya da harsashi biyar.

More from Tsaro