On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

2023: CP Gumel Ya Gayyaci Shugabannin NNPP Da APC, Gabanin Hukuncin Kotu Kan Zaben Gwamna A Kano

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mohammed Usaini Gumel, a ranar Alhamis, ya gayyaci shugabannin jam’iyyar NNPP da na APC, a wani taron zaman lafiya da aka shirya domin kawo karshen duk wata fargabar tashin hankali, gabanin yanke hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamna a jihar Kano zata yi.

 

Duubban magoya bayan jam’iyyar NNPP ne dai suka gudanar da addu’o’i na musamman a fadin kananan hukumomin jihar 44, a ranar Alhamis, inda suka nemi taimakon Allah domin samun nasara a kotun.

Da yake daukar matakan dakile duk wata barazana ko fargabar tashe-tashen hankula da ke kunno kai a tsakanin mazauna Kano, Kwamishinan 'yan sanda  Gumel ya gayyaci shugabannin jam’iyyun siyasar biyu a jihar nan domin taron sulhu.

Wata sanarwa da CP Gumel da kansa ya sanya wa hannu kan muhimman batutuwan ta nuna cewa shugabannin jam’iyyun siyasar biyu sun rungumi zaman lafiya tare da ba da tabbacin cewa za su amince da sakamakon da kotun ta yanke da zuciya daya.