On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

A Fara Duba Jinjirin Watan Zul Hijjah, Inji Sarkin Musulmi.

SARKIN MUSULMI

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulunci ta kasa , Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya umarci al’ummar Musulmi da su sanya ido kan ganin jinjirin watan Zul-Hijja daga gobe Laraba.

Abubakar ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin bada shawara kan harkokin addini na majalisar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Junaidu  ya  fitar  yau a  jhar  ta sokoto.

Sarkin Musulmi ya kuma umurci al’umma dasu kai rahoton ganin  jinjirin  watan  ga  Hakimai  ko  Dagacin ƙauye mafi kusa don sadarwa ga Sarkin Musulmi.

Zul-hijja shi ne wata na 12 kuma na karshe a cikin kalandar Musulunci da ake gudanar da aikin hajji mai tsarki, da kuma yin  layya.