On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

A Fara Duba Watan Ramadan Na 1444AH Daga Ranar Laraba

Mai alfarma sarkin Musulmin Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na III ya bukaci al’umma su fara duba sabon jin-jirin watan Ramadan daga gobe Laraba.

Sarkin musulmin ya bayyana haka ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan gudanarwa na majalisar koli ta harkokin addinin musulunci karkashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi.

Sanarwar ta ce, idan musulmi suka ga jinjirin watan a yammacin Laraba, to Sarkin Musulmi zai ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar farko ta watan Ramadan.

Ya kara da cewa idan ba a ga jinjirin watan a wannan ranar ba, to Juma’a za ta zama 1 ga  watan Ramadan.

More from Labarai