On Air Now

ZANGON SAFIYAR LAHADI

5:00am - Noon

A Yau Ne Kotu A Burtaniya Zata Yankewa Ekweramadu Hukunci

A yaune Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ike Ekweramadu tare da mai dakinsa Beatrice zasu san makomarsu, Yayin da wata kotu a Burtaniya zata yanke masu hukunci bayansu samunsu da lefin yunkurin cire sassan Dan adam ,domin yiwa yarsu mai suna Sonia magani.

Gabanin zartar da hukuncin, Wasu daga cikin fitattun ‘yan Najeriya dama kasashen Afrika na cigaba da yin kira ga  Kotun  data yiwa  sanatan  sassauci.

Kazalika suma majalisun dokokin kasar nan sunyi irin wannan roko a karshen makon jiya,  kamar  yadda  ita ma  wata kungiya  ta Ikeoha Mpu ta sake makamancin wannan kira.

Kungiyar  ta  bukaci kotun data  sassautawa  jagoran nasu wanda ya kasance  dan uwa  a gare su, ta hanyar  sakinsa  batare da gindaya wani sharadi ba.