On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

A Yaune Argentina Zata Kece Raini Da Crotia A Wasan Kusa Dana Karshe A Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa Ta Duniya

MESSI DA LUKA MODRIC

Mai horas da tawagar yan wasan kasar Argentina Lionel Scaloni ya tabbatar da cewa 'yan wasansa sun shirya tsaf domin buga wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya da kasar Croatia a yau.

Gwarzon dan wasan duniya  Lionel Messi na kasar  Argentina za su kara da fitaccen  dan wasan kasar  Croatia  Luka Modric a wasan kusa da na karshe, yayin da zakarun gasar a shekarar  2018 kasar  Faransa za ta kece raini  da Morocco a gobe.

Bayan shafe makwanni uku ana gasar a Qatar, kungiyoyi hudu ne suka rage a yayin da ake kan hanyar karkare  gasar .

Za'a take wasan ne daga karfe 8 Na dare agogon Najeriya