On Air Now

Off Air

Noon - 6:00pm

A Yaune Rukunin Farko Na ‘Yan Najeriya Daga Sudan Zasu Dawo Gida Najeriya.

ONYEMA

Matukar ba wani sauyi aka samu ba, Nan da 'Yan Sa’oi ne ake saran saukar rukunin farko na ‘yan Najeriyar da suka makale a kasar Sudan a birnin taraiyya Abuja, Kamar yadda Hukumar kula da ‘Yan Najeriya mazauna kasashen ketare NIDCOM ta baiyana.

Shugabar hukumar  Abike  Dabiri  Erewa wadda  ta bada  wannan tabbaci a daren jiya, Ta  ce  ofishin  jakadancin kasar nan dake Masar  ya samu nasarar  tsallakar  da  dukkanin ‘yan Najeriyar da suka makale akan  Iyakar  Arqeel  dake kasar Masar,  zuwa cikin kasar,  domin dauko su ta cikin jirgi zuwa  gida Najeriya.

Rahotanni sun baiyana cewar, Tuni jirgin rundunar  sojin sama ta kasa da kuma  na  Air  Peace da aka tura  zuwa kasar  ke dakon  akai masu mutanen  domin dauko su  zuwa  Abuja.

Kazalika  ta  ce  an bayar da kulawa  ta musamman  ga  Dalibai  mata, A  yayin da  ta  ce  za’a kwashe  sauran  mutanen  da suka makale a kan iyakar  Wadi  Halfa a safiyar  gobe  sannan  kuma wadanda suke kan iyakar  birnin Port Sudan, sune  zasu  zama na karshe  da za’a kwashe,  kasancewar  a jiya  ne suka karasa  wajen.