On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

A Yaune Sabbin Kudi Zasu Fara Zagayawa A Hannun Jama'a

SABBIN KUDI

Matukar ba wani sauyi aka samu ba, A yaune sabbin takardu kudi na naira 200 da 500 da kuma 1000 da aka sauyawa fasali zasu fara fita daga hannun bankunan ajiya zuwa abokan huldarsu.

Hakan yazo ne kimanin makwanni ukku bayan da shugaban kasa muhammadu buhari , ya kaddamar da sabbin takardun kudin a yayin taron majalisar zartarwa na mako-mako a fadarsa mulki ta Aso Rock Villa.

A cikin watan October ne, Gwamnan  babban bankin kasa  Emefiele ya bada sanarwar cewa bankin zai fara fitar da sabbin kudin a  yau, 15 ga watan Disambar da muke ciki.

Wata majiya daga bankunan ajiya, ta tabbatarwa  manema Labarai cewa, tuni bankunan ajiyar suka karbi sabbin takardun kudin tun kwanaki biyu da suka wuce, a saboda da haka daga yaune zasu fara raba su ga abokan huldarsu.

More from Labarai