On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

A yi Bincike Kan Zargin Cin Zarafin Dalibar Jami'ar MAUN - CAJA

Cibiyar Wayar da Kai da Tabbatar da Adalci ta Centre for Awareness on Justice and Accountability (CAJA) ta bukaci a gudanar da cikakken bincike kan zargin yunkurin cin zarafin wata daliba da ake yi wa wani malami a Maryam Abacha American University (MAUN) da ke Kano.

A cikin wata sanarwa da Jami'in Wayar da Kai da Sadarwa na cibiyar, Adam Auwal Dakata, ya sanya wa hannu, kungiyar ta bayyana damuwarta kan rahotannin da ke yawo game da lamarin, inda ta ce dole ne a gudanar da bincike cikin gaskiya da adalci.

CAJA ta ce cin zarafi a manyan makarantu na tauye mutunci, tsaro da 'yancin dalibai na neman ilimi cikin walwala. Ta kara da cewa irin wadannan zarge-zarge na iya rage amincin jama'a ga cibiyoyin ilimi idan ba a dauki matakin da ya dace ba.

Sai dai kungiyar ta jaddada cewa duk wanda ake zargi yana da hakkin a saurare shi cikin adalci, don haka ta bukaci a gudanar da binciken ba tare da nuna son rai ko bangaranci ba.

Kungiyar ta bukaci mahukuntan jami'ar su kafa kwamitin bincike mai zaman kansa wanda zai hada da wakilan jami'ar, malamai, lauyoyi, wakilan dalibai, kwararru kan kare hakkin mata da yara, da sauran mutane masu kwarewa da nagarta.

A cewar CAJA, ya kamata kwamitin ya gudanar da bincike cikin gaggawa tare da gabatar da shawarwarin da suka dace domin tabbatar da adalci bisa tanadin doka da ka'idojin jami'ar.

Har ila yau, kungiyar ta bukaci jami'ar ta tabbatar da kariya ga mai shigar da kara, shaidu da dukkan wadanda abin ya shafa daga tsoratarwa, cin zarafi ko ramuwar gayya yayin gudanar da binciken.

Baya ga wannan lamari, CAJA ta yi kira ga Maryam Abacha American University da sauran manyan makarantu a Jihar Kano da su samar ko kuma su karfafa manufofin yaki da cin zarafi, tare da samar da hanyoyin kai korafi cikin sirri, kare wadanda abin ya shafa da kuma hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Kungiyar ta kuma yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki su bai wa doka damar yin aikinta, tare da tabbatar da gaskiya, rikon amana da adalci domin kare martabar tsarin ilimi.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 34°C | Low: 22°C