On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Abba Kabir Yusuf Ya Kara Yin Sabbin Nade-Naden Mukamai

Gwamnan jihar kano, Alhaji Abba Kabir Yusif ya amince da yin karin wasu sabbin nade-nade har guda biyar, akan wasu mukamai daban-daban, a yayin da za’a yi bukin rantsar da mutanen nan bada jimawa ba.

Wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan na kano, Sanusi Bature ya fitar da Asubahin yau,  Ta  baiyana  sunayen mutanen da aka  nada  kan  sabbin mukaman,  wanda suka hada da Injinya Garba  Ahmed Bichi  a matsayin  Manajan daraktan  Hukumar Samar da Ruwan sha  ta  jihar Kano.

Sauran sune Dr. Rahila Mukhtar a matsayin Babbar Sakatariyar  hukumar kula shirin temakekeniyar  lafiya  ta jihar kano,  Sai  Hassan Baba  Danffa  a matsayin  Manajan Darakta  na hukumar   Gyaran   titina  ta jihar Kano, KARMA.

Ragowar  mutanen sune,  Arch. Ibrahim Yakubu  a  matsayin Manajan darakta  na hukumar  tsara birane ta jihar Kano  KNUPDA, sai kuma  Abdulkadir  Abdussalam wanda  ya zama  sabon babban akanta na jihar Kano.