On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Abba Kabir Zai Dawo Da Kadarorin Gwamnati Da Ake Zargin Ganduje Ya Sayarwa Iyalansa

Abba Kabir Yusuf

Shugaban kwamitin karbar Mulki na jam'iyyar NNPP Dr Abdullahi Baffa Bichi ne ya jagoranci kai ziyarar gani da Ido zuwa wajen da ake zargin an sayarwa da Abba Ganduje.

Gwamnan jihar Kano mai jiran Gado,Abba  Kabir  Yusuf Ya  ce  zai dauki matakin shari’a domin dawo da dukkanin wasu  kadarorin gwamnati da ake  zargin  gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje  ya sayarwa  iyalansa.
Da yake jawabi a ranar Laraba, Shugaban kwamitin dawo da kadarorin gwamnati, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin karbar  mulki na jam’iyyar  NNPP,  Dr Abdullahi Baffa Bichi, Ya  ce  ana zargin an sayar  da  hukumar  nan ta kula da kwangilolin gwamnati dake  kan titin state Road,  Ga  dan gidan gwamnan jihar Kano Abba Ganduje akan kudi naira  milyan 10.
Baffa Bichi ya kuma yi zargin cewar , Abba Gandujen  ya sayar da wurin akan kudi  sama da naira milyan 300, Inda  ya baiyana bacin ransa  kan irin halaiyyar da gwamnatin mai barin gado take nunawa,  ta hanyar  cefanar  da  kadarorin mallakin al’ummar jihar kano.
Duk da wani kokarin na jin ta bakin jami’an gwamnatin jihar Kano mai ci a yanzu domin maida  martani  kan zargin  bai samu nasara ba.
Sai dai idan ba’a manta  ba, Gwamna  Ganduje  ya  gargadi zababben  gwamnan jihar  kano  da  ya dena  azarbabi,  inda  y a  ce  ya bari  sai an rantsar  dashi a matsayin cikakken gwamnan jihar kano kafin daukar irin wannan mataki.