On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Abba Ya Mayar Da Muhyi Kan Mukaminsa Na Shugabancin Hukumar PCACC Ta Jihar Kano

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da mayar da Barista Muhyi Magaji Rimin Gado kujerar shugaban hukumar korafe-korafen Jama’a da yaki da cin hanci da rashawa, domin kammala wa’adinsa.

Idan za’a iya tunawa gwamnatin da ta shude ta dakatar da Barista Muhyi daga mukaminsa bisa wasu dalilai.

Sai dai wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamna Abba Kabir Yusuf, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta ce matakin maida Muhyi kan shugabancin hukumar ya fara aiki nan take domin bin Umarnin Kotu.