On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Abokan Huldar Bankuna Na Cigaba Da Kokawa Kan Karancin Takardun Kudi

Abokan huldar bankuna na cigaba da nuna bacin ransu sakamakon karancin takardun kudi, A yayin da bankuna da dama, suka takaita yawan kudin da mutum zai iya cira, su kuwa masu POS sun kara cajin da suke yi da kaso 100 bisa 100.

Ziyarar gani da ido da manema labarai suka kai wasu bankuna a Legas da Abuja, sunga yadda abokan huldar bankuna ke shan wahala wajen samun takardun kudi akan injinan cirar kudi na ATM, a yayin da mafi akasarin injinan basa  bada kudin.

Akwai dai dan karancin takardun kudi da bankuna ke fuskanta, sakamakon rashin samar masu  das u daga  babban bankin kasa, lamarin da  yasa bankunan suka rage  yawan tsabar kudin da mutum zai iya cira akan ATM ko kuma akan kanta.

A wani bangaren kuma, Babban bankin kasa  ya  dakatar da cajin  kudin da ake yiwa  abokan huldar bankuna masu ajiyar  kudi da yawa,  wanda zai kama naira dubu 500  ga masu asusun banki na kashin kai  ko kuma naira milyan ukku ga masu asusun ajiya  banki ta kanfanoni.