Jam'iyyar ADC ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi watsi da manufofin tattalin arzikin da ta bayyana a matsayin masu jefa 'yan Najeriya cikin talauci, ko kuma ya sauka daga mulki, tana mai cewa al'umma ba za su iya cigaba da jure wahalhalun da suke fuskanta ba.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labaran Jam'iyyar na Kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu a ranar Asabar, ADC ta bayyana damuwarta kan rahoton Bankin Duniya da ke cewa 'yan Najeriya miliyan 139 na rayuwa a karkashin ma'aunin talauci, tare da rahoton Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) da ya nuna cewa mutane miliyan 17 na fama da matsananciyar yunwa.
Jam'iyyar ta ce wadannan alkaluma hujja ce da ke nuna cewa manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu sun gaza, tana mai gargadin cewa idan aka cigaba da irin wadannan tsare-tsare bayan shekarar 2027, za su iya haifar da karin matsaloli ga kasar.
Ta ce cigaban tattalin arziki, karin kudaden shiga da habakar ajiyar kudaden waje ba su da amfani idan ba sa inganta rayuwar jama'a.
ADC ta ce idan aka zabe ta a 2027, za ta aiwatar da sauye-sauyen da za su magance tushen yunwa da talauci, ciki har da rage farashin makamashi, tabbatar da tsaron manoma da hanyoyin noma, farfado da madatsun ruwa 264 da aka yi watsi da su, fadada noman ban ruwa, inganta samar da iri da taki, da zuba jari a wuraren adanawa da sarrafa amfanin gona domin kara samar da abinci da inganta rayuwar 'yan Najeriya.
Comments
Add a comment