On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

ADC Ta Rushe Kwamitin Zartarwar ta a Kano

Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ta ƙasa ta rushe Kwamitin Zartarwa na jam'iyyar a Jihar Kano tare da ƙaddamar da Kwamitin Riƙon Ƙwarya da zai tafiyar da harkokin jam'iyyar har zuwa lokacin da za a gudanar da sabbin zaɓukan cikin gida.

Da take sanar da matakin a wani taron manema labarai, Mataimakiyar Shugabar Jam'iyyar ta Ƙasa mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, Hajiya Naja'atu Muhammad, ta ce an ɗauki wannan mataki ne bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam'iyyar da kuma Dokar Zaɓe, domin dawo da daidaito, tabbatar da cigaba, da kuma ƙarfafa tsarin jam'iyyar a Jihar Kano.

NAJA'ATU MOHAMMAD

Hajiya Naja'atu ta jaddada cewa kafa Kwamitin Riƙon Ƙwaryar ba yana nufin hukunta ko ƙasƙantar da gudunmawar mambobin jam'iyyar ba, tana mai yabawa dubban magoya bayan ADC da su cigaba da jajircewa wajen gina jam'iyyar tsawon shekaru.

Ta kuma yi kira ga shugabanni da mambobin jam'iyyar a dukkan ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano da su mara wa tsarin riƙon ƙwaryar baya, tare da fifita muradun jam'iyyar gaba ɗaya a kan muradun kashin kansu.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 35°C | Low: 24°C