On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Adesanya Na Najeriya Ya Doke Pereira Tare Da Sake Karbe Kambun UFC Na Matsakaita Nauyi

'Dan wasa Isra'il Adesanya ya doge Alex Pereira don sake samun kambun matsakaicin nauyi a babbar gasar UFC  a karshen mako.

Wannan dai shi ne karo na hudu da ake gwabzawa tsakanin ‘yan wasan biyu, inda Pereira ya doke Adesanya sau biyu  inda ya dauki kofin UFC.

Adesanya a karshe ya doke abokin hamayyarsa na tsawon lokaci.

Hakan na zuwa ne yayinda Zababben shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Ministan Wasanni Sunday Dare ke taya shaharerren dan Damban zamani na kasar, Israel Adesanya murna, bayan da ya kwace kambinsa na matsakaicin nauyi daga hannun dan kasar Brazil Alex Pereira a gasar UFC da suka fafata ranar Lahadi.

Adesanya ya yi waje da Pereira a zagaye na biyu na fafatawar da suka yi da sanyin safiyar Lahadi wajen kwato kambinsa da ya baras wa dan damben Brazil din  bara.

Tinubu ya taya shi murna ta shafinsa na Twitter jim kadan bayan nasarar. Haka shima Sunda Dare, yayi a nasa bangaren.