On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Ahmed Usman-Ododo Ya Zama Dan Takarar Gwamnan Jihar Kogi A Jam'iyyar APC

USMAN ODODO

A wani labarin kuwa, zaben fidda gwani na gwamna a jihar Kogi karkashin jam’iyyar APC da aka gudanar a jiya ya dauki wani sabon salo, yayin da mataimakin gwamnan jihar , Edward Onoja, ya janyewa babban bincike kudi na jihar, Ahmed Usman-Ododo takarar.

Wasu ’yan takara bakwai da suka hada da tsohon Kwamishinan Kudi, Mista David Adebanji-Jimoh  da  Asiwaju Ashiru Idris da Okala Yakubu, suma suma  sun janyewa Usman-Ododo   takarar  biyo  bayan amincewa  da takararsa  da Gwamna Yahaya Bello ya yi.

Sauran sun hada da Abdulkareem Asuku  wanda  shine  shugaban ma’aikata na gwamna  yahaya Bello da kuma Babban  Akantan jihar Momoh Jibrin.

Shugaban kwamitin zaben fidda gwani na jihar, Wanda kuma shine  gwamnan jihar  Zamfara, Gwamna Mohammed Bello-Matawale  shine  ya tabbatar da faruwar lamarin bayan zaben fidda  gwanin da aka gudanar  a jiya.